Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Cikin watanni 2 kacal mun kwace miyagun kwayoyi da kudin su suka kai naira biliyan 60 – Buba Marwa

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce cikin watanni biyu da suka gabata, ta samu nasarar kwace miyagun kwayoyi daban-daban da kudin su suka kai naira biliyan sittin.

 

Shugaban hukumar Burgediya janar Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a garin Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti.

 

Ya ce Najeriya a yanzu, babu babbar matsala da ta addabi jama’a fiye da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

 

‘‘Ko da rashin tsaro da ke addabar kasar nan a yanzu, musamman ayyukan boko haram da ‘yan bindiga da ke satar mutane suna garkuwa da su, duk suna alaka da ta’ammali da miyagun kwayoyi’’

 

Matukar mun dauki matakai musamman ta bangaren dakile hanyoyin da miyagun kwayoyin ke shiga hannun jama’a, za a rage matsalar da akalla kaso hamsin cikin dari’’  a cewar Buba Marwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!