Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Izala ta ƙaddamar da fara dashen Bishiyu a jihohin Arewa

Published

on

Ƙungiyar Izala ta ƙasa mai shalkwata a Kaduna ta ƙaddamar da shirinta na fara dashen itatuwa domin kare muhalli a jihohin Arewacin ƙasar nan.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Malam Abdullahi Balalau shi ne ya ƙaddamar da shirin a jihar Katsina. Ya ce, baya ga jihar ta Katsinan, ƙungiyar zata faɗaɗa shirin zuwa sauran jihohin arewacin ƙasar nan.

Malam Balalau ya ƙara da cewa, an gina birane ba tare da dashe ba, koguna suna gushewa hamada na gangarowa, ga ƙona daji, rayuwar mu na cikin hatsari.

Akwai barazanar cutuka su sake yaɗuwa, amma ta hanyar dasa itatuwa za a magance waɗannan matsaloli.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!