Labaran Wasanni
Jadawalin FIFA: Super Eagles ta koma mataki na uku a Afrika
Tawagar Super Eagles ta koma mataki na uku a nahiyar afrika, kuma mataki na 32 a jerin kasashe da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitarwa a kowane wata.
Super Eagles a watan da ya gabata ta kasance mataki na hudu a jerin kasashe a nahiyar afrika, wanda hakan ya sanya ta samu karin matsayi a jerin kasashen.
Wanda hakan ya nuna cewa Jerin kasashen ya sa kasar Senegal da ta lashe gasar kofin afrika na AFCON na shekarar 2021 da aka buga a shekarar 2022 a kasar Kamaru itace a matakin farko, kuma ta 18 a jerin kasashe a duniya.
Yayinda kasar Moroco ta kasance a mataki na biyu, sai kuma Najeriya a mataki na uku da kuma kasar Masar wato [Egypt] da Tunisia da Kamaru da Algeria da Mali da kuma Ivory Coast da suke a jerin jadawalin na FIFA.
Kasar Senegal dai ta zama zakara a gasar AFCON da aka kammala a kasar Kamaru a ranar shida ga Fabrairun shekarar 2022
Tawagar Algeria da itace ta farko a watan da ya gabata yanzu ta koma mataki na 43 a duniya, sai Mali ta 48 Ivory Coast kuma ta 51.
A jerin kasashen duniya kuma Belgium ce a matakin farko, sai Brazil, Faransa da Argentina da Ingila, Italy, Spain, Portugal, Denmark da kuma Netherlands wato Holland.
You must be logged in to post a comment Login