Addini
Jama’a su siffantu da halaye na kwarai -Malam Umar Hotoro
Na’ibin limamin masallacin Juma’a na Zam-Zam dake unguwar Hotoro, Malam Umar Mukhtar Hotoro, ya yi kira da jan hankalin al’umma wajen ci gaba da siffantuwa da halaye na kwarai don samun rabauta a wajen Ubangiji ta’ala.
Malam Umar Mukhtar Hotoro, ya yi kiran ne cikin Hudubar Sallar Juma’a da ya gabatar a masallacin.
Malamin ya ce ‘Shakka babu tausayawa tsakanin mawadata dake cikin al’umma zai taimaka, kuma Allah Subhanahu wata ala ka iya kallon wannan ayyuka don kawowa mutane kafatanin su sauki a cikin rayuwar su.
Malam Umar Mukhtar Hotoro, ya kara da cewa, akwai bukatar mutane su kaucewa ayyukan sabon Allah, kasancewar na daga cikin dalilan da Allah ke jarrabtar al’umma da musibu daban-daban.
Labarai masu alaka.
Killace kai da hana Sallah a cikin jama’a lokacin Annoba dai -dai ne a Musulunci
Limami: Sakacin koyarwar addinin musulinci shike kawo annoba
Malam Umar Hotoro ya ce ya zama tilas mutane su dauki shawarwarin likitoci da muhimmancin gaske, don zama kandagarki daga wannan annoba ta cutar Corona da ta game duniya baki daya.
Umar Idris Shuaibu wakilinmu da ya halarci masallacin, ya ruwaito cewar Na’ibin limamin masallacin karkashin cibiyar addinin musulunci ta Jama’atul Wa’azu Wal Irshad, ya bukaci masu wadata daga cikin mutane da su zage dantse wajen tallafawa marasa karfi don samun saukin rayuwa, kasancewar harkokin tattalin arziki sun yi baya matuka wannan hali da ake ciki na Annobar Corona.
You must be logged in to post a comment Login