Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Killace kai da hana Sallah a cikin jama’a lokacin Annoba dai -dai ne a Musulunci

Published

on

Babban Limamin Masallacin jumma’a na Alfurkan Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar , yace Killace kai da kauracewa al’umma, da karbar shawarwari na ma’aikatan lafiya da hukumomi dai -dai ne , a cikin koyar wa ta addinin Musulunci.

Dr Bashir Aliyu Umar , yace kasancewar addinin Islama tsari ne na rayuwa ba wai kawai addini ba, ya shirya komai daki – daki  da tsari na gudanar da mu’amala lokacin da Annoba ta sauka , don dakile yaduwa, kula da lafiya  da tsare rayuka na al’umma tare da dukiya.

Malamin  wanda ya bayyana haka a wata hira ta musamman da tashar Freedom Rediyo, ya kafa misalai , da Alkur’ani mai girma da Hadisai na Manzon Allah , wanda suka yi kira da Killace kai , tare da hana taro  shiga gari ko al’umma , a wajen addini da sauran al’amurra yau da kullum, wanda tsarin shari’a ya aminta dashi a matsayin babbar lalura.

Shehin Malamin, yace bai kamata al’umma su dinga karyata Annoba ba,   da yin halin ko in kula ta hanyar amfani da Addini, wajen yin biris da ka’idoji na killacewa wanda Musulunci ya yi horo dashi da kuma fatwa da dama akai.

Bugu da kari Malamin ,yace labarin da ake ta yadawa na cewar Yahudawa ne da Nasara suka kirkiri cutar don hana aiyyukan Ibadar Musulunci, labari ne mara tushe ballantana makama, kasancewar Turawa da Yahudawa na kan gaba -gaba wadan da cutar ta fi yiwa illa.

Dr Bashir Aliyu Umar, ya kuma yi kira da al’umma da su koma ga Allah, tare da tuba  kasancewar sai an saba masa ko an kauce fadin sa, Annoba ke sauka ga al’umma wanda su suka jawo ta da kansu sakamakon aiyyukan da suke aikatawa.

Ya kara da shawartar al’umma da su bi dukkanin matakai da shawarwari da ma’aikatan Lafiya da dangogin su suka bayar, tare da bin umarnin hukumomi don ganin an dakile ko kawar da cutar a fadin duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!