ilimi
Cacar baki: JAMB ta yiwa El-rufa’i martani
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantin ƙasar nan JAMB ta ce bata bayar da fifikon maki ga ɗaliban da suka rubuta jarabawar a yankin arewacin ƙasar nan.
Hukumar ta kuma ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bai yi daidai ba da ya ce ana sangarta ɗaliban Arewa da maki fiye da na yankin Kudancin ƙasar nan.
Shugaban sashinyaɗa labarai na hukumar JAMB, Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da jaridar PUNCH.
Wannan dai ya biyo bayan kalaman gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da yayi a cikin shirin gidan Talabijin na Channels ranar Litinin, inda ya ce bai kamata a riƙa fita maki ga yan Arewa fiye da takwarorin su na kudu ba, domin kuwa zai kara musu lalaci.
Benjamin ya ce JAMB ba ta taɓa saka mafi ƙarancin maki ga makarantu ba tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1978 a matsayin hukumar da za ta riƙa shirya jarrabawar bai wa dalibai damar shiga manyan makarantu a ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login