Labarai
JAMB za ta yi wa masu bukata ta musamman rijista kyauta
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Nijeriya JAMB, ta ce masu bukata ta musamman da ke son rubuta jarrabawar ta kakar 2024 zuwa 2025 za su iya yin rajista kyauta.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da rajistar masu sha’awar shiga jami’a a fadin kasar yau Litinin.
Farfesa Oloyede, ya kuma ce, hukumar ta JAMB za ta ba da takardun yin rijista kyauta ga dukkan nau’ukan masu bukata ta musamman a matsayin tallafi.
Haka kuma, ya bayyana cewa, an samar da matakan da za a tabbatar da gudanar da aikin ga dukkan dalibai, ya na mai bayar da tabbacin cewa za a samar da littattafan da masu lalurar gani za su yi amfani da su.
Shugaban na JAMB, ya kara da cewa, wannan ci gaban zai zo ne cikin nau’o’in sauti kamar MP3 da WMV da kuma WMA wanda zai dace da duk na’urorin da za su iya daukar bayanan sauti.
You must be logged in to post a comment Login