Connect with us

Labarai

Jami’an agaji na kokarin nemo mutane 40 da suka nitse a hatsarin kwale-kwalen Goronyo

Published

on

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan hatsarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Goronyo na jihar Sokoto.

 

Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasa tare da haɗin gwiwar hukumomin jihar suka bazama domin nemowa tare da ceto waɗanda suka ɓacen.

 

Waɗanda lamarin ya shafa yawanci ƴan kasuwa ne da suke hanyar tafiyar babbar kasuwar Goronyo da ke ci duk ranar Lahadi a lokacin da kwale-kwalen ya kife ɗauke da matafiya kusan 50, amma hukumomi sun ce an samu nasarar ceto mutum 10 daga ciki.

 

A makonni uku da suka gabata ne aƙalla mutum 13 suka rasu bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutum 100 ya kife a jihar Neja.

 

Haka kuma manoma 16 sun rasu a wani haɗarin a watan Agustan 2024 a jihar ta Sokoto, sannan a ranar 29 ga watan Yuli, ƴanmata shida sun nutse bayan kwale-kwale ya kife da su a jihar Jigawa.

 

Ko a kwanaki biyun da suka gabata, wasu mutum 13 sun mutu a haɗarin kwale-kwale a jihar Neja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!