Labarai
Jami’an CBN na ci gaba da canja wa mutane sababbin kudi a hannu
Majalisar masarautar Rano, ta buƙaci babban bankin ƙasa CBN da ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar nan.
Sakataren masarautar Alhaji Sani Haruna Rano, ne ya buƙaci hakan a yau lokacin da tawagar babban bankin ƙasa CBN ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Darakta a shalkwatar CBN da ke Abuja Engr Muhammad Alii, a ci gaba da aikin sauya wa al’umma kuɗi hannu da hannu.
Sakataren na masarautar Rano, ya ƙara da cewa, baya ga ƙara wa’adin, akwai buƙatar babban bankin ya ci gaba da wayar da kan al’umma musamman ma na karkara domin su rungumi tsarin sauya sababbin kuɗin.
A nasa ɓangaren, sakataren hakimin Tudunwada Alhaji Lamido da ya yi magana a madadin wakilin sarkin Rano Alhaji Bako Alu, yaba wa ya yi bisa tsarin yana mai cewa zai sauƙaƙa irin wahalhalun da al’umma ke fuskanta tare da yin kira ga mutane da su rungumi tsarin kai kuɗaɗensu bankuna domin kada su yi asara.
Shi kuwa Engr Muhammad Alii cewa ya yi sun je masarautar ne domin sauya wa mutanen tsofaffin kuɗin na adadin Naira budu 10 ga kowanne mutum, yayin da jami’an bankunan cikin tawagar za su buɗe wa masu fiye da Naira dubu 10 asusu da kuma bayyana hanyoyin da suke bi wajen sauya wa masu buƙata ta musamman da kuma ɗaurarru kuɗin.
Zuwa daren yau Laraba, tawagar ta CBN ta gudanar da aikin caja kuɗin a garin Riruwai da Doguwa da Tudunwada, kuma Rano.
Rahoton: Auwal Hassan Fagge
You must be logged in to post a comment Login