Labarai
Jami’an tsaro sun garkame fadar Sarkin Kano
Jami’an tsaro sun garkame fadar mai martaba sarki Kano Malam Muhammadu Sunusi na II biyo bayan tsige shi da gwamnatin Kano tayi a dazu.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa an giciye kofar fadar sarkin da motar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano.
Yayin da al’umma suka yi dandazo a kofar fadar sarkin suna nuna jimamin su kan matakin na tsige sarkin Kano.
You must be logged in to post a comment Login