Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Firaministan Sudan ya tsallake Rijiya da baya

Published

on

Firaministan kasar Sudan Abdolla Hamdak, ya tsallake rijiya da baya, a wani yunkurin kisa da aka kai masa a yau din nan ta hanyar tada Bom a jerin gwanon motocin sa lokacin da yake tafiya zuwa ofishin sa da safiyar yau  a birnin Khartoum.

Firaminista Hamdok, ya tabbatar da labarin afkuwar hakan  ta shafin sadarwar sa na  twitter, in da yace ‘ina nan lafiya cikin kwanciyar hankali bayan yunkurin harin na yau’.

Ya kara da cewa abinda ya faru ba zai sa suyi kasa a gwiwa ba wajen ganin an tabbatar da juyin juya hali da kasar ke bukata ba, sai ma dan ba da suka saka a halin yanzu.

Firaminista Hamdok, ya saka hotunan sa yana murmushi a ofishin sa jim kadan bayan komawar sa, tare da labarin talabijin din kasar ke gudanarwa  na yunkurin kisan da akayi masa a yau din.

labarai masu alaka.

 An zargi DPO da hannu wajen kisan kai

A ranar 19 ga watan Maris shekarar 2007 ne shugaba Umar Hassan Al-Bashir ya musanta zargin cin zarafin bil’adama

Kawo yanzu ba a samu kungiya ko wani  wanda suka dau alhakin kai harin ba, wanda ya lalata motoci guda biyu tare da fasa gilasan wasu da dama daga cikin jerin gwannon motocin dake rufawa Firaminista Hamdok baya.

Ministan yada labarai na kasar ta Sudan, Falih Salih, a ce yanzu haka ana fadada bincike don gano su waye suka kitsa abun tare da kai harin da niyyar kashe shugaban.

Abdollah Hamdok, ya karbi jagorancin kasar ne bayan da doguwar zanga zanga, da ‘yan kasar suka shafe suna gudanarwa ta tafi da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir, wanda sojoji suka hambarar da gwamnatin sa a watan Afrilun shekarar data gabata.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!