Labarai
Jami’an tsohuwar gwamnatin Sudan sun tsere da gidan Yari
Rahotonni daga kasar Sudan, sun bayyana cewa, mafi yawa daga cikin jami’an tsohuwar gwamnatin ƙasar da ake tsare da su kan tuhumar laifukan yaƙi sun tsere daga gidan yarin birnin Khartoum.
BBC ta ruwaito cewa, wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin da ke gwabza faɗa suka amince da batun tsagaita wuta na kwanaki 3.
haka kuma ta bayyana cewa, babban jami’in majalisar dinkin duniya a Sudan Volker Perthes, ya ce, lamarin ya ƙara tabarbarewa.
Haka kuma kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a New York ya na ta kira ga sojojin gwamnati da na RSF kan su ajiye makamai.
Mista Perthes ya shaida wa jakadun ƙasashen biyu ba su shirya tattaunawar sulhu ba.
Cikin waɗanda suka tsere akwai Ahmad Haroun wanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo.
You must be logged in to post a comment Login