Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta kama matasa 83 da ake zargi da kwacen waya a Kano

Published

on

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama matasa 83 da ta ke zargi da aikata fashi da makami a lokacin bukukuwan sallah karama
  • Matasan da aka kama an kamasu ne a cikin lunguna da sako na Jihar Kano
  • Yayin da wasunsu aka kamasu suna siyar da miyagun kwayoyi
  • Rundunar ‘yan sandan ta ce ‘da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu’

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama matasa 83 da ta ke zargi da aikata fashi da makami a lokacin bukukuwan sallah karama.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan, ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio a daren jiya.

Wanda ya ce ‘matasan da aka kama an kamasu ne a cikin lunguna da sako na Jihar Kano, wadanda yawancinsu aka kamasu da makamai a hannunsu, suna yunkurin yiwa mutane fashi na wayar hannu’.

‘Yayin da wasunsu aka kamasu suna siyar da miyagun kwayoyi ga ire-iren matasan da ake zargin da fashi da makamin’.

‘Haka zalika rundunar ta samu nasarar karbar kayayyaki a hannunsu da suka hadar da wayoyin hannun, jakakkunan mata, da na’u’rar kwamfuta a hannun  matasan’.

Sai dai rundunar yan sandan ta ce, da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu.

 

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!