Kiwon Lafiya
Jami’ar Bayero ta bukaci mahukunta su cigaba da amfani da takardun SUKUK don ciyar da al’umma gaba
Jami’ar Bayero da ke nan Kano ta bukaci hukumomi a dukkanin matakai da su ci gaba da yin amfani da takardun lamuni da babu ruwa a ciki da ake kira da Sukuk domin ciyar da al’umma gaba.
Daraktar cibiyar hada-hadar kudi da banki a mahangar addinin musulunci ta kasa-da kasa da ke jami’ar ta Bayero IIIBF Farfesa Binta Tijjani Jibril ce ta bayyana hakan yayin gabatar da mukala mai taken sayar da takardun lamuni da babu ruwa a ciki domin ciyar da al’umma gaba daya gudana jiya a jiami’ar Bayero da ke nan Kano.
Farfesan Fatima Jibril ta ce an gudanar da mukalar ne domin a wayar da kan al’umma da hukumomi muhimmancin sayar da takardun lamuni na Sukuk da babu ruwa wadanda kuma suka yi dai-dai da koyarwar addinin musulunci.
Ta kuma ce yadda ake sayar da takardun na sukuk kowa na da ikon siyasa duba da karancin kudaden da ake sayar da takardun na lamuni.
Da yake gabatar da mukala yayin taron Ba’amurke Dr Manzur Kahf ya bayyana cewa muhimmancin da takardun lamunin na Sukuk ke da shi a cikin harkar al’amuran kudi na musulunci, inda ya ce ya kamata gwamantoci a dukkan matakai su rungumi al’amuran na SUKUK.s