Labarai
Jami’ar Bayero ta Kano ta yaye sababin likitoci 68
Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya shawarci sabbin Likitocin da jami’ar ta yaye da su zama jakadun jami’ar na gari musamman wajen ciyar da bangaren lafiya gaba a fadin Najeriya.
Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana hakan ne lokacin da jami’ar Bayero ta Kano ke gudanar da bikin yaye sabbin dalibai Likitoci sittin da takwas da jami’ar ta gudanar a yau a harabar makarantar.
Muhammad Yahuza Bello wanda ya sami wakilcin Farfesa Bala Nasidi Aliyu ya kuma taya sabbin Likitocin murna kan nasarar da suka samu.
Yayin da kuma ya bukaci sabbin Likitocin dasu gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da kuma tsoran Allah cikin aikin su.
BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa
BUK ta kori dalibai 63 saboda satar jarrabawa
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Likitoci ta kasa shiyyar Kano shawartar sabbin Likitocin yayi dasu sadaukar da kansu ga aikin hidimtawa al’umma su kuma gudanar da aikin su cikin kwarewa domin tallafawa al’umma kamar yadda suka dauki alkawari.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito malaman jami’ar Bayero da dama ne suka halarci bikin yaye sabbin Likitocin na yau da sauran ‘yan uwa da abokan arziki domin tayasu murna kan nasarar da suka samu na zama likitoci.