Labarai
PDP ta kalubalanci gwamnatin Nijeriya kan salonta na kayyade mafi karancin albashi
Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Nijeriya ta kalubalanci gwamnatin tarayya bisa bayyanar wata takarda da ke nuni da yadda aka bukaci baiwa kwamatin da gwamnatin ta kafa tare da dora masa alhakin kayyade mafi karancin albashi a kasar.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP ta kasa Debo Ologunaba ne ya bayyana kalubalantar matakin, inda yace ‘bai kamata a ware wadannan makudan kudade ga kwamatin ba, a daidai lokacin da al’ummar kasar ke cikin halin kuncin matsin rayuwa’.
Ta cikin takardar data bayyana ba tare da sanin mahukunta ba, an gano yadda sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya rubuta takardar neman baiwa kwamatin har naira miliyan dubu ga shugaban Kasar Tinubu, tare da bada tabbacin kammala aikin kwamatin zuwa watan Afrilu.
To sai dai kuma wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce naira miliyan dari biyar ne shugaba Bola Ahmad Tinubun ya amince da baiwa kwamatin bayan gabatar masa da takardar.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login