Labarai
Jam’iyyar APM ta ce Tinubu ba zai samu kuri’u a Arewa ba

Jam’iyyar adawa ta APM ta gargadi shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya sa ran samun kuri’un al’ummar arewacin kasar nan, a zaben 2027, tana zarginsa da cin amanar yankin.
Daraktan yada labarai da dabarun sadarwa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Richard Ihediwa, ne ya bayyana hakan yayin da jam’iyyar APC ke shirin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a yau Asabar a jihar Kaduna.
Ihediwa ya zargi gwamnatin Tinubu da aiwatar da manufofin da ya ce sun jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin mawuyacin halin tattalin arziki.
Ya bayyana cewa wadannan matakai na daga cikin dalilan da suka sa jam’iyyar ke ganin bai kamata shugaban kasar ya dauka cewa zai samu goyon bayan masu zabe a arewa ba.
You must be logged in to post a comment Login