Labarai
Za a samu karin wutar lantarki a Kano – TCN

Gwamnatin tarayya ta ce za’a samu karin lantarkin da zai habbaka tatalin arzikin jihar Kano sakamakon kayan lantarki na zamani da ta samar.
Ministan lantarki na Kasa Joseph Tegbe, ne ya bayana hakan a ziyarar bude wasu ayuka da gwamnatin tarayya ta samar a tashar lantarki ta TCN dake Unguwar Dakata, Walalambe, Dan agundi da kuma babbar tashar lantarkin dake Gaida cikin karamar hukumar kumbotso a nan Kano.
Kamfanin dakon Wutar Lantarki na TCN ya kuma girka manyan na’urorin wutar lantarki masu ƙarfin gaske a tashar Kumbotso.
Cikin jawabinsa da harshen turanci Ministan ya kara da cewa kamfanin ya kuma sa na’urar wutar lantarki mai ƙarfin 100MVA 132/33kV a tashoshin Dan’Agundi da Dakata, tare da gina sabuwar tashar isar da wutar lantarki mai na’urori biyu, kowacce mai ƙarfin 40MVA 132/33kV, a Wallalambe.
A nasa jawabin shugaban kamfani tunkudo lantarkin na kasa TCN Shiyar Kano Injiniya Muhammad Kamar Bello cewa yayi sabin naurorin da aka kadamar zasu kara saukaka ayukansu tare da kara yawan wutar lantarki ga kamfanoni da Unguwanni.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa taron kadamar da aikin ya samu wakilcin Gwamnatin jihar kano da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin lantarki a matakin jiha da kuma kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login