Kiwon Lafiya
Jam’iyyar PDP ta ce munafinci ne ayyana ranar goma sha biya a ga watan Yuni a matsayin ranar demokradiya
Jam’iyyar PDP ta ce munafunci ne kawai ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar goma sha biyu ga watan Yuni a matsayin ranar dimukuradiya.
Ta kuma ce karrama Abiola a wannan lokaci ba wani abu bane face neman suna don biyan bukata ta siyasa.
Mai Magana da yawun jam’iyyar Kola Ologbondiyan, ya ce; shugaba Buhari wanda ya yi aiki da gwamnatin mulkin soji ta janar Sani Abacha wanda a lokacin Abiola yana daure kuma bai ce uffan ba, a don haka yanzu siyasa ce kawai ta sa shi daukar wannan mataki.
Ya ce, da tun a waccan lokacin da gwamnatin mulkin soji karkashin jagorancin Sani Abacha wadda ta yi shura wajen cin zarafin Abiola ya nuna damuwarsa, to da kuwa ba ko shakka za su ya ba da matakin da ya dauka a yanzu.
A wani bangare kuma gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode, ya bayyana ayyana ranar goma sha biyu ga watan Yunin a matsayin wani abin tarihi da ba za a manta da ita ba a tarihin siyasar kasar nan har abada.
Gwamna Ambode ya ce ba kowane shugaba ne yake da karfin guiwa da zai iya daukar wannan mataki ba, a don haka ya ce tarihi ba zai manta da shugaba Buhari ba.
Yayin da anata bangaren gwamnatin jihar Ogun wanda nan ne mahaifar Abiola ta jinjinawa shugaba Buhari kan daukar matakin da ta ce ya gagari wasu a baya.