Connect with us

Labarai

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin da zai shirya babban taronta na kasa 

Published

on

Jam’iyyar PDP ta kafa kwamitin da zai shirya babban taron ta na kasa  karkashin gwamman jihar Adamawa Amadu Fintiri.

 

PDP ta ce majalisar zartarwar ta amince da kafa wani karin kwamitin da zai yi nazari a kan tsarin karba karban mukamai a jam’iyyar gabanin babban taronta, a karkashin Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri.

 

Jamiyyar ta dauki wannan mataki ne a yayin zaman majalisar koli da ta gudanar a ranar Talata a Abuja.

 

A yayin taron, jam’iyyar ta kuma yi Alla-wadai da rufe shelkwatarta da hukumar kula da birnin Abuja ta yi, tare da shan alwashin bin kadin matakin.

 

A ranar Litinin hukumar kula da birnin Abuja, ta garkame shelkwatar PDP da aka fi sani da Wadata Plaza saboda rashin biyan haraji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!