Labaran Kano
Jam’iyyar YPP ta kori jagoran jam’iyyar daga mukamin sa
Majalisar zartaswar jamiyyar Youth Progressive Party YPP ta jihar Kano ta kori tsohon shugaban jamiyyar na riko Ibrahim Sadauki Kabara sakamakon zargin cin Amana da rashin gaskiya da saba dokokin jamiyyar.
Barista Salisu Salisu Umar , ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar , yana mai cewa majalisar zartaswar jamiyyar ta dauki matakin ne biyo bayan saba dokokin jamiyyar da tsohon shugaban yayi wanda kuma ya saba da kundin tsarin mulkin jamiyyar.
Majalisar zartaswar jamiyyar ta kuma amince da nada Barista Salisu Salisu Umar a matsayin sabon shugaban na Jihar Kano domin dorawa daga inda aka tsaya.
OSUN:kotu ta karyata ikrarin jam’iyyar PDP
Taraba:Darius Ishaku na jam’iyyar PDP ya lashe zabe
Barista Salisu Salisu Umar ya kuma shawarci matasa da kada su bari ‘yan siyasa marasa kishi suna amfani dasu wajen tayarwa da jama’a hankali lokacin yakin Neman Zabe , dama amfani dasu wajen zabar mutanan da basu kamata ba domin sune ke jefa kasar nan cikin mawuyacin hali.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Barista Salisu Salisu Umar na shawartar al’ummar Kano da su cigaba da adduar neman dorewar dimukaradiyya a fadin kasar nan.