Kiwon Lafiya
Janar Ibrahim Badamasi Babangida : ya danganta rikicin addini da kabilanci ne ya mamaye demokradiyar kasar nan
Tsohon shugaban mulkin Sojin kasar nan Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya danganta shekaru 19 na tsayayyen mulkin Dimokradiyya a matsayin wanda rikicin addini da kabilanci ya mamaye.
Ibrahim Babangida ya ce abin damuwa matuka yadda ‘yan-siyasar kasar nan ke take doka da kin bin tsarin Siyasa yadda ya dace, yana mai cewa tun daga ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999 zuwa yanzu Jam’iyyun siyasa basu da wasu nagartattun manufofi.
Haka zalika babu abinda ake gani face sauyin shekar ‘yan-siyasar daga Jam’iyyu zuwa wasu Jam’iyyun baya ga rikicin cikin gida daya addabi Jam’iyyun.
Sannan ya bayyana cewalokaci ya yi da ya kamata a ce an mayar da hankali wajen gina Jam’iyyun Siyasa guda biyu kwarara a kasar nan, musamman ma a wannan yanayi da babban zabe ke karatowa.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata da aka rabawa manema labarai mai kunshe da sa-hannunsa, inda ya ce tun bayan samun ‘yan-cin kan kasar nan a shekarar 1960, kasar ta fuskanci rikice-rikice da tashin hankali iri-iri, a don hak babu wani kuduri da ya kamata a baiwa fifiko face dunkulewar kasar nan waje guda.
Kana kuma akwai bukatar girmama juna tare da martaba ra’ayin kowa ba tare da cin zarafi ko cin mutuncin kowa ba.