Labarai
Jigawa: Ƴan sanda sun musanta rahoton ɓullar ƴan bindiga a Dutse

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna cewa, an ga wasu ‘yan bindiga suna kutsawa cikin garin Dutse a cikin dare .
A cewar rundunar, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne, face mambobin ƙungiyar mafarauta daga Jihar Bauchi, waɗanda suka fito daga wani taro da suka halarta a karanar hukumar Ringim kafin a ɗauki bidiyon.
Rundunar ta bukaci jama’a da su yi watsi da bidiyon baki ɗaya, tana mai gargadin cewa irin wannan labari na ƙarya wanda ka iya haifar da tashin hankali da firgita jama’a ba tare da wani dalili ba.
Ta cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, Kwamishinan ƴan Sandan Jihar ta Jigawa Dahiru Muhammad, ya buƙaci mutane da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, yana kuma kira da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro rahotonni na gaskiya kan duk wani motsi ko mutumin da ba su yarda da shi ba.
You must be logged in to post a comment Login