Labarai
Jigawa ce ta fi kowace jiha wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da yin fyade- Shugaban ICPC

Shugaban hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya ICPC Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN ya ce jihar Jigawa ce ta fi kowace jiha wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata fyaɗe a duk faɗin Najeriya.
Dakta Musa Adamu Aliyu, ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki da kungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA a birnin tarayya Abuja.
A cewar sa, daga shekarar 2019 zuwa 2023 jihar Jigawa ce kan gaba inda ta fi samun masu aikita laifukan fyade.
Haka kuma shugaban na ICPC, ya bukaci lauyoyi da su kara jajircewa wajen tabbatar da ana yanke wa masu aikata laifukan fyade hukunci dai-dai da abinda suka aikata.


You must be logged in to post a comment Login