Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Autan AliCoron Virus ya sha kaye

Published

on

AUTAN ALI (Coron Virus) ya sha kaye.

 

Shahararre Dan  Damben nan Autan Ali, da aka fi sani da Coruna Virus, ya sha kaye a wasan sa na 60 da ya yi kokarin kafa tarihi bayan nasara 59, daya samu a baya.

Bayan shafe Wasanni 59,  cikin samun galaba akan abokanan hamayyar sa ,  Autan  Ali Coronavirus, ya sha kasa a hannun  Dandabatula,wanda ya kasheshi a turmi na  uku bayan saka turmi biyu ana fafatawa.

Rashin nasarar tashi, tasa bai samu damar kafa tarihin wasanni 60, ba tare da an buge shi ba, sai dai duk da haka dan wasan ya kafa tarihin buga wasa 59, ba tare da an samu galaba a kansa ba wanda yake sabon abu ne a Damben gargajiya a Arewacin kasar nan.

DAMBE: Bahagon Wada ya lashe kyautar mashin

‘Yan damben Arewa da kudu sun dambata a Kano

Wasan dai an fafata shi ne jim kadan, kafin a buga   wasan karshe na gasar cin mota na  kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Alhaji Kabiru Lakwaya, wanda aka Dambata shima a yammacin Lahadi a filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabongari.

Sai dai wasan karshen na cin gasar Motar an tashi ba wanda ya samu nasara, tsakanin Alin Bata isarka daga Kudu da Autan Dan Bunza daga Arewa, wanda aka saka turmi biyar babu kisa.

Bayan warwarewar zaren Alin Bata isarka an tsaida wasa ,wanda tsaikon yasa aka dage Damben  sai mako mai zuwa ranar Lahadi in da za’a  fafata don samun Zakara.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!