Labarai
Jihar Neja ta bi sahun sauran Jihohi wajen samar da sabbin matakan tsaro

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya fitar da sabbin matakan tsaro wanda ya hada da rufe manyan kasuwannin da ke ci mako-mako a fadin jihar.
Kazalika Gwamnatin ta taƙaita lokutan babura inda masu babur za su riƙa hawa daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma. Sannan kuma an hana motocin ita ce zirga-zirga a fadin jihar.
Sakataren Gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya yi ƙarin bayani a kai, inda yace hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a jihar.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara suma suka sanar da ɗaukar wannan mataki.
You must be logged in to post a comment Login