Labaran Wasanni
John Terry ya bar Aston Villa don neman aikin manaja

John Terry ya bar matsayinsa na mataimakin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa bayan shafe shekaru uku a kungiyar.
Terry mai shekaru 40, yazo Villa ne a matsayin dan wasa a shekara 2017 har zama kyaftin.
Ya buga wasanni 32 a kungiyar a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 kafin daga baya ya zama mataimaki ga mai horarwa Dean Smith a watan Oktoban 2018.
Terry ya taimakawa Smith wajen samun ci gaba a gasar Championship a watan Mayun 2019.
You must be logged in to post a comment Login