Ƙetare
Juyin mulki: ƙasashen larabawa sun buƙaci mayar wa farar hula mulki a Sudan
Ƙasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bi sahun kawayensu na ƙasashen yamma wajen kira ga sojin ƙasar Sudan da suka karbe iko da su gaggauta mayar da mulki ga gwamnatin farar hula.
Wannan dai na zuwa ne bayan da a baya ƙasashen na larabawa da ke da kyakykyawar alaƙa da dakarun sojin Sudan ɗin, ba su yi wata kwakkwarar magana a kan karbe ikon da soji suka yi a kasar ba.
A sanarwar hadin gwiwa da suka fidda, sun bukaci da a gagauta sakin duk wadanda ake tsare da su sakamakon juyin mulkin, da ma janye dokar ta bacin da sojin suka saka a kasar.
Haka zalika, Kasar Amurka ta bukaci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta kara matsa kaimi ga sojojin Sudan din da su saki hambararen firaminista Abdallah Hamdok daga daurin talala da suke ci gaba da yi masa a gida.
Al’ummar kasar Sudan na adawa da matakin karbe iko da sojojin suka yi, lamarin da ya kai su ga hawa tituna domin zanga-zangar lumana da ta yi sanadiyar rasa rayukan wasu daga cikinsu.
You must be logged in to post a comment Login