Ƙetare
Juyin mulki – AU ta dakatar da Sudan daga cikin mambobin ta

Ƙungiyar tarayyar Afirka ta dakatar da ƙasar Sudan daga cikinta har sai an dawo da mulkin farar hula a ƙasar.
Ƙungiyar ta ce juyin mulkin da sojoji suka yi ranar Litinin ya saɓawa kudin tsarin mulki.
Tun bayan juyin mulkin ne zanga-zangar nuna ƙin jinin juyin mulkin ke ci gaba da gudana a birnin Khartoum tsawon kwanaki 3 a jere.
You must be logged in to post a comment Login