Kiwon Lafiya
Kaciyar da ake yiwa mata na haifar musu matsaloli yayin haihuwa-Dr. Zainab Datti
Wata kwararriyar Likita a bangaren Cututtukan da suka shafi mata, Dokta Zainab Datti Ahmad, ta bayyana cewa shayi da ake wa ‘ya’ya mata na daya daga cikin babban kalubalen da ke haifarwa mata matsaloli yayin haihuwa.
Dakta Zainab Datti Ahmed wadda Likita ce a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, ta bayyana hakan ne yayin zantawa da ita jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Rediyo, a wani bangare na bikin yaki da yiwa ‘ya’ya mata kaciya da ake gudanarwa a Talatar nan.
Kwarariyar likitar ta kara da cewa matan da aka yiwa shayin na kamuwa da wasu cutuka da suka shafi zubar da jini da matsanincin ciwon mara.
Dokta Zainab Datti Ahmad ta ce kamata ya yi gwamnati ta kara kaimi wajen kirkiro shirye-shiryen da za su rika wayar da kan mutane dangane da illolin da ke tattare da yi wa ‘ya’ya mata shayi .
Zainab Ahmed ta kuma shawarci iyaye da su guji yiwa ‘ya’yan su mata kaciya don magance matsalolin da suke samu yayin zamantakewar aure.