Labarai
Kai tsaye: ‘Yan sanda na bai wa masu sayar da wayoyin hannu horo a Kano
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da hadin gwiwar kwamitin kyautata alaka tsakanin ‘yansanda da jama’a sun fara bayar da horo ga masu sayara da wayoyin hannu.
Taron na yini guda ne wanda ke gudana a wurin shakatawa na manyan Yansanda dake Unguwar Bomfai.
Masu sana’ar sayar da wayoyin hannu daga sassa daban-daban na jihar Kano sun halarci taron.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Freedom Radio cewa, an shirya taron ne domin a wayar da kan masu sana’ar sayar da wayoyin.
Ya ce, za nusar dasu kan yadda zasu kaucewa fadawa tarkon masu sayen kayan sata.
Da kuma yadda za su rika bai wa hukumomi hadin kai wajen gano batagari musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar kwacen wayoyi.
You must be logged in to post a comment Login