Labaran Wasanni
Kaka-tsara-kaka: Barcelona ko Bayern Munich, wa zai samu nasara a wasan yau?
A yau Juma’a ne dai kungiyoyin Barcelona da Bayern Munich za su kece raini a wasan daf da kusa da na karshe wato (quarter final) a gasar zakarun turai.
Duk kungiyar da ta samu nasara a wasan na yau, za ta fafata da ko dai Manchester city ko kuma kungiyar Lyon a wasan daf da na karshe wato (semi Final).
Wasannin baya-bayan nan da kungiyoyin biyu su ka yi a tsakaninsu a gasar ta zakarun turai, shine a kakar shekara ta 2013/14. A wasan dai Bayern Munich ta ci zarafin Barcelona, inda ta casata da ci bakwai da nema gida da waje (7-0).
A wasan farko da aka yi a ranar 23 ga watan Afrilu a shekarar 2013 a filin wasa na Allianz Arena da ke birnin Munich, Bayern Munich ta lallasa Barcelona da ci hudu da nema (4-0), sannan ta biyo ta a zagaye na biyu a filin wasa na Camp Nou da ke birnin Barcelona a kasar ta Spaniya, ta doketa da ci uku da nema (3-0), jimilla gida da waje bakwai kenan da babu.
Sai dai shekara daya bayan faruwar wannan lamari, Barcelona ta samu galaba akan Bayern Munich da ci biyar da uku a wasan gida da waje da suka yi. Da farko dai Barcelona ta doke Munich a da ci uku da nema a filin wasa na Allianz arena da ke kasar Jamus kafin daga bisani ta yi rashin nasara da ci uku da biyu a filin wasa na Camp Nou da ke kasar Spaniya.
Haka zalika masu lura da harkokin wasanni na ganin cewa, hankalin ‘yan kallo zai koma kan ‘yan wasan gaba na kungiyoyin biyu, wato Leonel Messi da Robert Lewandowsky.
Lewandowsky dai shine dan wasa da ke kan gaba a gasar a yawan zura kwallaye inda yanzu haka yak e da kwallaye goma sha hudu tare da taimakawa a zura a raga har sau uku.
Shi kuma dan wasan Barcelona Leonel Messi yana da kwallaye bakwai sannan ya taimaka an zura guda tara.
Wani batu da zai ba da sha’awa kan wannan wasa shine ganin cewa dukkannin masu tsaron raga na bangarorin biyu Jamusawa ne wato Golar Bayern Munich Manuel Neuer da na Barcelona Marc-Andre ter Stegen.
Koma me zai kasance Allah ne masani, amma an jima kadan za a banbance tsakanin aya da tsakuwa.
You must be logged in to post a comment Login