Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Shekaru Goma Sha Shida Kenan Cif Da Kafa Kamfanin Da Yafi Nigeria Arziki

Published

on

Daga Abdullahi Isah

A rana irin ta yau hudu ga watan Fabrairu a shekarar dubu biyu da hudu wani hazikin matashi mai suna Mark Elliot Zuckerberg, ya kaddamar da wata manhajjar shafin sada zumunta wanda ya radawa suna ‘Facebook’.

Wannan matashi dai tare da tallafin wasu abokansa da su ke zama daki daya a Jami’ar Havard da ke kasar Amurka ya kaddamar da wannan fasaha ce a cikin  dakin su na makaranta.

Tun daga waccan lokaci zuwa yanzu Kamfanin Facebook sai kara bunkasa ya ke an Kuma fara tallata hannayen jarinsa a shekarar dubu biyu da goma sha biyu.

A yanzu dai kadarorin wannan Kamfani na Facebook ya kai dala biliyan dari da talatin da uku da miliyan dari uku da sabain da shida.

Hukumar kula da kamfanoni sadarwa ta ce ta gano yadda ake cirewa kwastamomi kudade babu gaira babu dalili

A shekarar da ta gabata ta dubu biyu da goma sha Tara Kamfanin Facebook ya ci ribar dala biliyan sabain da miliyan dari shida da casa’in da bakwai. Bugu da kari, Kamfanin Facebook ya na da maaikata dubu arba’in da hudu da dari tara da arba’in da biyu.

Haka zalika Kamfanin Facebook shine ya mallaki wadannan kamfanoni: Instagram da Messenger da WhatsApp da Watch da Portal da Oculus da Kuma Calibra.

Kamfanin Facebook dai yana da shalkwata a Menlo Park da ke jihar California a kasar Amurka.

Kowane darasi matasan kasar nan zasu koya game da wannan matashi da ya kafa wannan katafaren Kamfani? Wannan dai tambaya ce mai saukin amsawa sai dai Kuma fahimtarta ita ce babban abin dubawa.

A tawa Fahimtar babban darasi da ya kamata matasa su koya kan Kamfanin Facebook da Kuma Mark Zuckerberg da ya kirkiro dashi shine Fahimtar cewa ilimi zai iya sa wa mutum ya mallaki kowane irin dukiya a duniya. Domin a yanzu Mark Zuckerberg yana cikin manyan attajirai na duniya guda ashirin da suka fi dukiya a duniya.

Haka zalika shine mafi karancin Shekaru cikin wadannan manyan attajirai, sannnan babu abinda ya yi sanadiyar hakan face ilimi.

Idan aka kwatanta dukiyar ajiya na kasar nan da ke ketare a karshen watan Disamba shekarar da ta gabata, kasar nan tana da sama da dala biliyan talatin da takwas, yayin da a bangare guda Kamfanin Facebook ke da kadarar sama da dala biliyan dari da talatin da uku yayin da  Mark Zuckerberg ya mallaki sama da dala biliyan tamanin. Wannan karara ya nuna cewa Kamfanin Facebook ya fi kasar nan dukiya.

Ba ya ga dukiya Kamfanin Facebook ya taka rawa wajen mai da duniya wata ‘yar kankanuwar kauye inda yanzu jama’a ke sanin abinda ya faru a Kowane sassa na duniya cikin kankanin lokaci.

Ba ko shakka Kamfanin Facebook  a yanzu ya saukaka hanyoyin yada labarai da sada zumunci ba ya ga zama wata kafa na samar da aikin yi ga dumbin jama’a a duniya.

Masu sharhi kan harkokin tattalin Arziki sun yi ittifakin cewa a yanzu Facebook kusan shine kan gaba wajen samar da aikin yi a duniya baki daya.

Tabbas duniya za ta dade  ba ta manta da irin gudunmawar da Mark Zuckerberg ya bayar ba wajen sauya rayuwar alummar duniya sakamakon fasahar da ya kirkiro.

Muna taya Kamfanin Facebook murnar cika Shekaru goma sha shida da kafuwa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!