Kasuwanci
Kamfanin Twitter ya amince da sharuddan da gwamnatin tarayya ta gindaya masa
Kamfanin Sadarwa na Twitter ya amince da dukkan sharudan da aka gindaya masa kafin ya ci gaba da aiki a kasar nan.
Ministan yada labaran Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin.
Lai Muhammad ya ce, kamfanin Twitter na ci gaba da tattaunawa da gwamnati tare da samar da matsaya wajen ci gaba da ayyukan su a kasar nan.
A cewar Lai Muhammad, tuni shugabanin kamfanin suka amince da matakan da aka gindaya musu, tare da alkawarta mutunta ikon Najeriya, da kula da muhimman abubuwa da suka shafi tsaron kasar da hadin kai kafin dawo da shi.
Idan za a iya tunawa gwamnatin tarayya ta dakatar da amfani da shafin Twitter tun a ranar 5 ga watan Yunin 2021 sakamakon goge wani rubutu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafin sa.
You must be logged in to post a comment Login