Kiwon Lafiya
kamfanoni 30 ne suka aike da bukatar karbar jinginar ma’aikatar albarkatun ruwa
Ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa ta ce kawo yanzu ta karbi takardun kamfanoni 30 daga hukumar dake kula da alamuran jingine kadarorin gwamnati ta kasa kan batun jingine madatsar ruwa ta Gurara.
Ministan albarkatun ruwa Suleman Adamu ne ya bayyana hakan, yayi da yake karbar takardun kamfanonin da suke sha’awar shiga tsarin a jiya Litinin a Abuja cewa, wannan babban nasara ce kasancewar bangare mai zaman kan sa ya shiga shirin jinginar da madatsar ruwan na Gurara wajen sarrafa ruwa don samar da wutar lantarki a Najeriya.
Suleman Adamu ya ce nan gaba kadan majalisar zartarwa ta kasa zata amince da batun jinginar da madatsar ruwan na Gurara, yana mai cewa kofar ma’aikatar a bude take wajen karbar takardun kamfanonin dake da sha’awa wajen jinginar da madatsarun.
Da yake jawabi babban daraktan hukumar dake kula da lamuran jirginar da kadarorin gwamnati ta aksa Chidi Izuwah ya yabawa ma’aikatar wajen sanya gaskiya a yayin da za’a jinginar da madatsar ruwan na Gurara.