Labaran Kano
Kannywood ta fara mayar da martani kan matakin hana sanya Fina-fanai a manhajar Youtube
Darakta kuma mashiryin Fina-finan Hausa a Kanyywodd Kamal S. Alkali ya mayar da martani kan matakin da hukumar tace Fina-finai da dab’i ta jihar kano ta dauka na hana sanya fina-finan a manhajar Youtube.
Kamal S. Alkali ya ce wannan mataki ba zai haifar da “da” mai ido ba face kara jefa matasa cikin rashin aiki yi.
Har ma ya ce “duk duniya babu wata kasa da ke tsauarara matakin ta ce abubuwan da za a sanya a cikin mmanhajar ta youtube”.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan da hukumar ta sanar da cewa daga yanzu ta hana sanya Fina-finai a Youtube matukar ba a tace su ba, kamar yadda mukaddashin babban jami’I mai kula da shiyyara Arewa maso Yamma ya bayyana.
You must be logged in to post a comment Login