Labarai
Kano : Abubuwa bakwai da Ganduje ya fada akan Abduljabbar Nasiru Kabara
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce daga yanzu ya fara daukar mataki kan kalaman batanci ga Annabi da Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi, tare da nuna isgilancin ga addinin musulunci.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis ya yin da yake jawabi ga malamai da limamai na jihar Kano dangane da kalaman da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke yi na tunzura Jama’a akan fiyayyen halitta.
- Hudubar Limamai ta mayar da hankali wajen Kalaman batanci da Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi.
- Gwamnati ba zata zuba Ido tana ganin ana kalaman batanci ga fiyayyen halitta ba.
- Gwamna Ganduje ya ce “Wannan matakin yanzu ma mu ka fara dauka. Akwai abubuwan da za su biyo baya.”
- Da can mu na ta jin abubuwan da ake fada sai mu ka ce a kawo mana hujja akan hakan, “Mu na samun hujja sai mu ka dauki mataki kamar yadda a ka fara gani.”
- Ya kamata a kara nunawa al’umma munin wannan babban al’amari da Abduljabbar ke aikatawa.
- “Wannan hobbasa, ba ta gwamnati ba ce ita kadai. Ta mu ce gaba daya. Babban abin haushin ma shine, bayan karuwar faruwar irin wannan abu, sai ya zamana ma cewar abin ya na ma kara zurfi. Idan a ka yi la’akari da yadda wannan abin ya faru.”
- Sa’annan ya kara da cewa zai ci gaba da zama da Malaman saboda tuntubarsu kan yadda abin zai dinga tafiya. Ya kuma kara neman goyon bayan al’umma da ci gaba da yi wa jihar ta Kano addu’o’i kamar yadda a ka saba yi.
Abunda wasu malaman Kano suka ce kan matakin Ganduje :
Ka zalika wasu daga cikin malaman da suka yi jawabi a ya yin taron sun ce ba sa bukatar Muqabala da wanda ya yi batunci ga Annabi Muhammad , Sallallahu Alaihi Wasallam.
Sakon Mai alfarma sarkin Musulmi da Wazirin majalisar masarautar Katsina:
A jawabinsa na bude taro da takaitaccen bayani, Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahar Adam, ya bayyana irin sakonnin da su ke samu daga jama’a daban daban na yabawa da wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka.
Ya ce, ”Sarkin Musulmi da Wazirin Katsina sun aiko da sakon jinjina ga Gwamna Ganduje kan matakin da ya dauka akan Abduljabbar Nasiru Kabara”.
You must be logged in to post a comment Login