Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da ya sa Ganduje ya rufe masallacin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara a Kano

Published

on

Sakamakon rahotanni da aka samu dangane da kalaman na tunzura Jama’a da ka iya kawo tashin hankali da sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke yi  majalisar zartarwar Kano ta umarci da a gaggauta rufe masallaci da cibiyar da yake gudanar da karatukansa a filin mushe da ke nan Kano.

Ka zalika Majalisar zartarwa ta Kano ta ce sai  jami’an tsaro sun kammala binciken da suke gudanar wa a halin yanzu kan malamin bisa  furta kalaman tunzura jama’a a ya yin da yake gudanar da wa’azi a masallacin sa.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya bayyana hakan a daren jiya a fadar gwamnatin Kano ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Malam Muhammad Garba ya kara da cewa, majalisar zartarwa ta Kano ta kuma umarce shi sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da  ya dakatar da wadannan wa’azi da yake yi wanda ka iya kawo rudani da tashin hankali a nan Kano da ma kasa baki daya.

Majalisar ta kuma umarci kafafen yada labarai dana sada zumunta da su dakatar da sanya karatuttukan sa don tabbatar da samun zaman lafiya a jihar Kano

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa, gwamnatin ta Kano ta kuma umarci jami’an tsaro da daukar matakin gaggawa kan duk mai irin wadannan kalaman anan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!