Labaran Kano
Kano : Akalla manoman alkama dubu dari ne za su sami tallafi a bana
Gwamnatin jihar Kano tace sama da Manoman Alkama dubu dari ne zasu sami Tallafin Noman a shekarar bana.
Mai taimakawa mataimakin gwamna Kano, a fanin yada labarai kan harkokin gona Bashir Idris ungogo ne ya bayyana hakan, lokacin da kwamitin binciken yadda manoman Alkama ke gudanar da noman su da irin Kalubalen da suke fuskanta ke zagayen tuntubar manoman a yau.
Bashir Ungogo , ya ce a baya manoman alkama sun fuskanci kalubale, wanda hakan ya sanya gwamnati ta fito da kyakyawan tsarin da zai inganta noman na su tare da bunkasa tattalin arzikin jiha.
A nasa jawabin shugaban manoman Alkama na jihar Kano, Alh. Musa Shehu, cewa ya yi, sama da Hekta dubu dari uku da sittin ake da ita a nan jihar Kano, da za a iya nomawa sai dai kawo yanzu Noman Alkamar bai wuce Hekta dubu dari ake Nomawa.
Rubutu masu alaka :
Manoma 450,000 a Kano zasu amfana da tallafin Noma
Shirin bunkasa noma da kiwo na jiha zai hada kai da cibiyoyin bincike
Wasu daga cikin Manoman Alkaman ciki har da Mata daga kananan hukumomin da aka ziyarta, sun yi karin haske kan matsalolin da suke fuskanta akan Noman Alkamar.
Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, dake cikin tawagar zagayen ya ruwaito cewa Kwamitin a yau, ya ziyarci kanana nan hukumomin Gezawa da Gabasawa da Ajingi da kuma karamar hukumar Gaya.
You must be logged in to post a comment Login