Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: An cafke ƴan adaidaitar sahun da suka shirya zanga-zanga

Published

on

Ƴan sanda sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da shirya zanga-zangar masu baburan adaidaita sahu a Kano.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan.

Ya ce, sun kama mutane biyun ne suna raba takardu domin gayyatar masu adaidaita sahu su shiga zanga-zanga a ranar Litinin.

Kiyawa ya gargaɗi duk wasu masu yunƙurin shirya wata zanga-zanga da su kaucewa hakan domin gudun tayar da hankalin jama’a.

Ya kuma ce, ƴan sanda sun shirya tsaf domin daƙile duk wani yunƙuri da zai kawo rashin zaman lafiya da sunan zanga-zanga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!