Labarai
Kano: An naɗa masu bada shawara kan gidajen kallo da nishadi
Shugaban karamar hukumar Ungogo Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya amince da nadin manyan masu bashi shawara guda ashirin.
A cikin wata sanarwa mukaddashin sakataren karamar hukumar ta Ungogo Baffa B Chiroma ya fitar a jiya juma’a, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Wadanda aka nadan sun hada da: Kamal Ibrahim babban mai ba da shawara kan fasahar zamani, Abdurrashid Lawan mai ba shawara kan kungiyoyi masu zaman kansu, Abdulaziz Wane-wane mai ba da shawara kan shirin tallafawa matasa, Abubakar Musa Dansiba babban mai ba da shawara akan ilimi mai zurfi, Bello Musa mai ba da shawara akan masu saye da sayarwa
Sauran sune: Usman Adamu Galadima mai ba da shawara kan hada kan jama’a, Shuaibu Umar Gayawa babban mai ba da shawara na biyu kan hada kan jama’a, Hadiyatullah Abdurrahman babban mai ba da shawara kan hada kan matasa, sai kuma Tijjani Bachirawa babban mai taimakawa shugaban karamar hukumar kan gidan kallo.
A bangare guda akwai: Abubakar Muhd, mai ba da shawara kan wasanni, Usman Coach Gayawa babban mai ba da shawara kan harkokin wasanni na biyu, Imam Umar mai ba da shawara kan asibitin dabbobi.
Haka zalika akwai: Auwal Abdussalam wanda aka nada a matsayin mai ba da shawara kan maganin gargajiya, Na’umma Ladan mai ba da shawara kan noman rani, Ibrahim Liti babban mai ba da shawara kan noman rani na biyu, Kwamared Na’iya Tudun Fulani babban mai ba da shawara kan hada kan matasa na biyu.
Sanarwar ta kuma ruwaito sunusu DJ Boss a matsayin babban mai ba da shawara kan nishadi, Rabi’u Adamu mai ba da shawara kan harkokin siyasa ta gabas, Yahaya Ali B-Mota mai ba da shawara kan Makabarta yayin da Musa Tijjani ya kasance mai ba da shawara kan dangantaka tsakanin kananan hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login