Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Kano: Ana zargin kuɗin marayu miliyan 345 sun yi ɓatan dabo daga asusun kotunan shari’ar Musulunci

Published

on

Rahotanni daga hukumar lura da kotunan musulunci ta jihar Kano na cewa an shiga ruɗani sakamakon zargin ɓatan dabon kuɗaɗen marayu.

Bayanai sun nuna cewa zunzurutun kuɗi har miliyan ɗari uku da arba’in da biyar ne suka yi layar zana daga lalitar kuɗaɗen marayun da ke shari’a a kotunan.

Babban magatakardar hukumar Sheikh Haruna Khalil ya tabbatarwa da Freedom Radio lamarin.

Ya ce “Tuni an kafa kwamitin bincike domin diddigi, sannan ƙorafin yana gaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kano”.

 

Yaya aka yi kuɗin suka ɓace?

Sheikh Haruna Khalil ya ce, kuɗaɗe ne na magada da kotunan musulunci ke ajiyewa a bankin Stanbic IBTC, amma da aka je domin neman wani kaso a ciki, sai aka tarar wayam an wawashe saura miliyan tara.

Ya ƙara da cewa, ana zargin wasu da har yanzu ba a san ko su waye ba, sun riƙa zarar kuɗin ta hanyar amfani da sa hannun bogi, na wasu manyan hukumar da ke da ikon fitar da kuɗin.

 

An sace na’urorin Kwamfiyutar da ake adana bayanan hada-hadar kuɗaɗe a hukumar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan kafa kwamitin bincike an samu wasu sun sace Kwamfiyotocin adana bayanan kuɗi na hukumar ta lura da al’amuran kotunan musuluncin ta Kano.

 

Alƙalin alƙalan Kano ya tabbatar da faruwar lamarin

Dr. Tijjani Yusuf Yakasai shi ne alƙalin alƙalan Kano ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, sun miƙa maganar ga hukumar yaƙi da rashawa ta Kano.

 

Mun yi nisa a binciken lamarin – Anti Kwarafshin

Shugaban riƙon hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Kano Barista Mahmud Balarabe ya ce, sun yi nisa wajen bincike kan wannan al’amari.

Ya ci gaba da cewa “Mun gayyaci masu ruwa da tsaki a kai, tun daga ma’aikatan hukumar har zuwa jami’an bankin na Stanbic IBTC”.

 

Me bankin IBTC ya ce a kai?

Freedom Radio ta tuntuɓi manajan bankin Stanbic IBTC Malam Kabiru Ƙiru amma ya ce, ba shi da alhakin ya ce komai, sannan ba shi da hurumin ya haɗa mu da waɗanda ke da alhakin yin magana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!