Connect with us

Labarai

Kano: Ana zargin yaro ya rasu sakamakon cutar Diphtheria

Published

on

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta jihar Kano ta bayar da rahoton mutuwar wani yaro mai shekara 11 a ƙauyen Gawo, da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada, bayan ya nuna alamun cutar Mashako watau Diphtheria.

 

Rahoton binciken da hukumar ta fitar a ranar 21 ga Oktoba, 2026, ya ce an kwantar da yaron mai suna Usaini Nasir a asibitin kula da cutuka masu yaɗuwa na Kano IDH a ranar 12 ga Oktoba, bayan ya fara nuna alamun cutar.

 

An shawarci mai kula da shi da ya gudanar da gwajin ɗakin bincike domin tabbatar da cutar.

 

Sai dai rahoton ya ce mai kula da yaron ya bar asibitin tare da shi zuwa gida, kafin daga bisani yaron ya rasu a ranar 21 ga Oktoba.

Hukumar ta ce binciken da aka gudanar a yankin bai gano wasu mutane masu nuna irin waɗannan alamomin cutar a halin yanzu ba. Sai dai an fara bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da yaron, ciki har da ‘yan gidansu da sauran makusantansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!