Labarai
Atiku ya bukaci gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yadda aka kashe Biliyan 10 da aka ware don magance Ebola

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta yi cikakken bayani kan yadda aka kashe Naira biliyan 10 da aka ware domin shirin tunkarar cutar Ebola.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan sanar da samun mutuwar mutum guda da ya kamu da cutar a babban birin nin tarayya Abuja, yana mai cewa lamarin ya haifar da tambayoyi kan yadda gwamnati ta shirya tunkarar cutar da kuma yadda aka gudanar da shirin.
Ya bukaci gwamnati ta bayyana adadin kuɗin da aka saki da yadda aka kashe su, da kuma kayayyakin da aka saya domin kare lafiyar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login