Connect with us

Labarai

FRSC ta gargadi jami’anta kan su guji bin yan siyasa yayin yakin neman zaɓen 2027

Published

on

Hukumar kiyaye afkuwar Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta ce, ta gargadi jami’anta da su guji bin ’yan siyasa yayin yakin neman zaɓen shekarar 2027.

 

Jami’ar hukumar mai kula da shiyya ta RS6, Mataimakiyar Kwamanda ta Corps, ACM Abimbola Owolabi, ita ce ta bayar da wannan umarni yayin ziyarar aiki ta farko da ta kai hedikwatar hukumar ta jihar Cross River da ke birnin Calabar.

 

Owolabi ta bayyana cewa ba za a yi amfani da motocin sintiri na hukumar wajen harkokin siyasa ko wasu al’amura na kashin kai ba, ciki har da bukukuwan aure da jerin motocin masu zuwa jana’iza.

Ta umurci jami’an da aka tura wuraren da ake gudanar da kamfen da su mayar da hankali kawai kan kula da zirga-zirgar ababen hawa, domin hana CInkoson ababen hawa da kuma rage haɗurran hanya.

Haka kuma, ta buƙaci jami’an da su ƙara wayar da kan jama’a game da kiyaye dokokin hanya, tana mai cewa ci gaba da gudanar da irin waɗannan shirye-shirye na iya taimakawa wajen rage haɗurra da cimma burin kawar da mace-mace sakamakon haɗurra.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!