Connect with us

Labarai

Babbar kotun Kano ta yanke hukuncin kisa ga matasan da su ka kashe matar aure da yayanta 6

Published

on

Babbar kotun jiha da ke Bompai karkashin jagorancin Mai Sharia Nasir Saminu, ta yanke wa Umar Auwal da Yakubu Dayyabu  hukuncin kisa bayan Samun su da laifin kashe matar auren nan Fatima Abubakar da kuma yayanta 6a Unguwar Chiranci.

 

Kotun ta yi wannan hukuncin ne a yau Juma’a bayan da ma su gabatar da kara Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma kwamishinan Sharia Barista Abdulkarim Kabir Maude tare da rakiyar lauyoyi su ka bayyana a gaban kotun.

 

Yayin da a daya bangaren, Barista J.I Musa shi ne ya jagoranci lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma.

 

Haka kuma, Mai Sharia Nasir Saminu, ya wanke Isyaku Dayyabu Cobe daga wannan zargin kisan iyalan.

 

Sai dai wakilin namu ya shaida mana cewa mijin matar da matasan su ka kashe bai halarci zaman kotun ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!