Labarai
Kano: Ganduje ya kirkiri shirin koyar da dalibai daga gida
Gwamnatin jihar kano ta ce zata fara koyar da dalibai ta kafar Radio da talabijin, sakamakon rufe makarantu da tayi a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Corona.
Kwamishinan Ilimi na jihar kano Alhaji Muhammad Sanusi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Alhaji Muhammad Sanusi ya ce koyar da yaran zai bada dama yaran su cigaba da karatunsu daga gida.
Ta cikin sanarwar ta bayyana cewa a dai dai lokacin daliban Kananan ajujuwan makarantar sakandire ke shirye shiryen zana jarabawa, mai maimakon su zauna a gida kawai zasu amfani da damar wajen cigaba da karatun su.
Alhaji Muhammad Yace zasu mayar da hankali ne wajan koyawa daliban darusan Ingilishi da kuma Lissafi da kuma sauran da rusa.
You must be logged in to post a comment Login