Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Gombe ta yabawa wasu matasa kan COVID-19

Published

on

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya yabawa wasu matasa su uku kan yadda suka samar da na’urar samar da iska na gida wanda za’a yi amfani da shi wajen yaki da cutar Corona.

Gwamnan na Gombe ya ce yabawa matasa ya zama wajibi kasancewar sun kirkiru na’urara da zata taimakawa gwamnati wajen yaki da cutar COVID-19.

Alhaji Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da maitaimaka masa kan kafafan yada labarai Isma’ila Uba Misilli ya fitar a birnin Gombe.

Ta cikin sanarwar Gwamnan ya yi alkawarin Gwamnatin sa zata taimakawa matasan wajen cimma nasarorin su don ganin mafarikin su ya zama gaske.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!