Labaran Kano
Kano: Gwamnati ta musanta zargin barkewar COVID-19
Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarun da ake yadawa a shafukan sada zumunta wanda ke bayyana cewa an samu bullar Annobar Coronavirus a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta fitar wadda jami’ar yada labaran ma’aikatar Hajiya Hadiza Namadi ta sanyawa hannu, cewa gwamnatin ta ce, labarin da ake yadawa ba shi da tushe-balle-makama.
Sanarwar ta ce wasu marasa kishin Jihar Kano ne suka yi amfani da shafukan bogi na BBC da CNN wajen yada wannan labarin don tayar da hankalin jama’a.
A don haka ne ma kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bukaci al’umma da su yi watsi da jita- jitar wadda ba komai zata haifar ba illa rashin zaman lafiya a Jihar Kano.
Kananan hukumomin Kano sun shirya yakar COVID 19
Covid-19: Gwamnatin Kano ta bada umarnin rufe makarantun Allo dana Islamiyya
Covid-19: NMA ta bukaci membobinta da suka tsindima yajin aiki da su dawo aiki
Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya shawarci mutane da su mayar da hankali wajen daukan matakan kare kai daga kamuwa da cutar da suka hadar da wanke hannu da gujewa shiga cunkoson jama’a tare da kai rahoton duk wasu alamu da da aka gani a tattare da wani da ba’a amince da shi ba, sanar da jami’an kiwon lafiya, don daukar mataki nag aba.
You must be logged in to post a comment Login