Labarai
Kano: Kotu ta umarci ƴan sanda su biya diyyar Naira Miliyan Goma
Kotun tarayya mai lamba biyu da ke Kano ta umarci ƴan sanda su biya diyyar Naira Miliyan Goma ga dangin ɗaya daga cikin matasa biyu da suka kashe.
Yayin zaman kotun na yau Jumu’a mai shari’a Muhammad Nasir ya yanke wannan hukunci tare da gargaɗin ƴan sandan kan ɗaukar doka a hannu.
Tun da farko lauyoyin masu ƙara Barista Ahmed Musa da Muhammad Salahu sun shigar da ƙara gaban kotun suna neman a biya diyyar Naira Miliyan Ɗari.
Idan zaku iya tunawa a ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar 2020 ne, aka zargi ƴan sandan sashen Anti Daba da yiwa matasan biyu Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman kisan gilla a unguwar Sharaɗa.
Gidan rediyon Freedom ne ya fara kwarmata wannan labari, wanda kuma ya ɗauki hankulan al’umma da dama.
Ku saurari rahoton wakilin Freedom Radio Abubakar Tijjani Rabi’u a wancan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login